Shugaban Kwamitin Babban Birnin Tarayya (FCT), Sanata Dino Melaye, ya bayyana cewa ya kamata Buhari ya san cewa Majalisar Dattawa fa da ta Tarayya ba wasu ofisoshin da ke karkashin sa ba ne, balle ya ce sai yadda ya ga dama zai jujjuya su.
Melaye yayi wannan jawabi ne kwana daya bayan da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi jawabin cewa Majalisa ta yi wa kasafin 2018 zaftaren kudade kuma ta yi azururun wasu kudaden da wasu ayyuka.
“Wato ni abin da na fahimta shi ne, shugaba Buhari na kikiniyar wanke kansa ne a idon ‘yan Najeriya, a lokaci guda kuma ya na shafa mana bakin fenti.
“Abin da fa kawai doka ta ce wa shugaba ya yi, shi ne ya kawo mana kasafin kudi a Majalisar Kasa. Abin da ya kawo din nan kuwa bai zama doka ba, har sai mun duba shi mun yi abin da ke aikin mu, wato yin gyare-gyare. Mu din ma abin da doka ta ba mu umarnin yi kenan.”
Melaye ya kara da cewa babu inda doka ta ce da Buhari ya kawo kasafin kudi, shikenan sai su amince da duk abin da kowane minista ya rubuta zai kashe kawai a sa hannu kasafi ya zama doka.
Daga nan sai Dino ya ce, kuma me ya sa har ya yi azarbabin sa wa kasafin hannu idan ya na da korafi? Sannan daga baya ya fito ya na babatun bata wa ‘yan Majalisa suna kuma? Ya ce ai ba wanda ya tilasta shi cewa sai ya sa hannu.
A karshe Melaye ya nuna bacin rai yadda ake tafiyar da kasafin kudi tun shekaru uku kenan lokacin da Buhari ya hau mulki.
Ya ce ikon da Majalisa ke da shi, babu wani shugaba da ya isa ya kankare musu shi.