Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta bayyana cewa sama da jam’iyyun siyasa 100 ne ake sa ran za su fito takarar mukamai daban-daban a zaben 2019.
Shugaban Hukumar ne, Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana haka a wani taron wayar da kai da wasu kungiyoyi suka shirya ga masu ruwa da tsakin zabe jiya Alhamis a Abuja.
Kungiyar Kula da Batutuwan Zabe ta TMG, sai kuma DFID da V2P ne suka shirya taron.
Yakubu ya ce ya zuwa yanzu jam’iyyu 138 ne suka nemi a yi musu rajista a matsayin jam’iyyun siyasa.
Baya ga wannan kuma, ya bayyana cewa jami’an kula da shige-da-fice sun damke bakin-haushe ‘yan wata kasa sama da 300 da aka kama sun a kokarin yin rajistar damar kada kuri’a a Najeriya.
“Ya zuwa ranar 24 Ga Mayu, an samu karin yi wa mutane miliyan 9 rajista a kasar nan. Wannan ya karo adadin wadanda ke da rajista a Najeriya sun kai kimanin milyan 80 kenan.
“INEC ta na hada kai da karfi da jami’an tsaro domin dakilewa da bincike da damke masu sayen kuri’u da kudin a lokacin da ake zabe.” Inji Yakubu.
A karshe ya ce INEC ba ta da karfin ikon da za ta hana kowace kungiya fitowa ta yi rajistar zama jam’iyya, matukar dai ta cika sharuddan da doka ta gindaya na yin rajistar jam’iyya.
Idan ba a manta ba, a farkon wannan shekara, INEC ta tabbatar da cewa yawan jam’iyyun siyasa ba zai kawo wa hukumar wani cikas yayin gudanar da zaben 2019 ba.
Discussion about this post