Allah ya yiwa Sarkin Fadan Kano kuma tsohon minister Alh Sule Gaya rasuwa a daren Alhamis.
Kwana biyu da suka wuce Mai Girma Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ya kai masa ziyarar gaisuwar sallah kamar yadda ya saba duk shekara, kuma Ya jagoranci addu’o’in Allah kara masa lafiya.
Sarkin fadan Kano ya rasu yana da kimanin shekaru 92 a duniya, iyalan sa za su sanar da shirye shiryen jana’izar sa wadda ake sa ran yi a Yau a garin Kano.
Mai Girma Gwamna Ganduje a madadin sa da gwamnatin sa, na mika sakon taaziya ga iyalan marigayin da kuma ma al’ummar jihar Kano baki daya. Da fatan Allah sa Ya huta, Allah sada shi da Rahamar sa, Ya kuma yi masa sakaiya da gidan Aljanna, amin.
Mun samu wannan Sanarwa ne daga Tanko Yakasai, Kakakin gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje.