An samu karuwar yawan masu fama da yunwa a duniya – UN

0

Majalisar Dinkin duniya ta ruwaito cewa mutane miliyan 815 na fama da yunwa a duniya.

Majalisar ta gano haka ne a binciken da ta gudanar a shekarar 2017 inda ya nuna cewa an sami karuwar yawan mutanen dake fama da yunwa a duniya daga miliyan 777 a shekarar 2015 zuwa miliyan 815 a 2017.

” Wannan karuwa da aka samu a duniya na da nasaba da rikici, canjin yanayi da cinkoson jama’a a birane.”

Game da nasarorin da aka samu a shirin MDGs UN ta ce har yanzu ana fama da ganin an kauda zazzabin cizon sauro, tsaftace muhalli, da rashin dakunan bahaya.

Share.

game da Author