Rundunar sojin Najeriya ta sanar cewa daya daga cikin sojojin da dake bakin daga a yaki da Boko Haram da ake yi a karamar hukumar Mafa jihar Barno ya harbe kansa da bindigar sa.
Rudunar ta bayyana cewa hakan ya faru ne ranar 18 ga watan Yuni inda sojan da gangar ya juya bindigar sa sannan ya dirka wa cikin sa harsa shi.
Rundunar ta ce wannan soja ya fito ne daga bariki da ke jihar Kwara.
” Ya zo jihar Barno cikin koshin lafiya inda ya karbi bindigarsa sannan ya kama hanyar zuwa Mafa wurin sauran ‘yan uwan sa sojoji.”
” A lokacin da yake wurin mun sami labarin cewa sojan ya so harbe wani mai kula da dakin adana kaya, da ya samu ya tsira sojan ya dirkawa kan sa harsashi.”
Rundunar ta ce sojan ya rasu bayan an kai sa asibitin ‘7 Division Medical Centre’ dake Maiduguri.
Bayanai sun nuna cewa yakin da sojojin ke yi da Boko Haram ya sa wasu daga cikin su sun fara samun tabuwar hankali, domin a kwanakin baya wani soja ya harbe kansa da wani kaftin haka kawai.
Ana nan ana ci gaba da bincike akan abin da ya faru.