Abinda za ayi a gama da Boko Haram – Ali Ndume

0

Sanata Ali Ndume dake wakiltan Barno ta kudu a majalisar dattawa ya lissafo wasu wurare da rundunar sojin Najeriya za ta maida hankali sosai idan har tana so ta kawo karshen Boko Haram kwata-kwata.

Ya ce wadannan wurare suna yankunan kananan hukumomin Damboa/Gwoza/Chibok da yankin tafkin Chadi

Ndume da yanzu haka na kasar Saudi wajen aikin Umrah ya ce dole sai an maida hankali wadannan wurare ne fa za a sami nararar cewa an gana da Boko Haram.

Idan ba a manta ba wasu ‘yan kunan bakin wake shida sun tada bamabamai a garin Damboa a daidai mutane ke dawowa daga sallar Idi ranar Juma’a.

Rundunar Sojin Najeriya ta ce mutane 31 ne suka rasa rayukan su sannan 48 sun sami rauni a dalilin wannan hari.

” Ina da labarin cewa shugaban wannan kungiya Abubakar Shekau na jagoran bangare kungiyar daga Chibok ne sannan Mamman Nur na jagoran sauran bangare kungiyar da ga tafkin Chadi ne.” Inji Ndume.

Share.

game da Author