Wata matan aure mai suna Hassana Angyan ta nemi kotun dake Kubwa ta raba auren ta da mijinta mai suna Abdullahi Angyan saboda karya wasu dokokin addini da yake yi da suka shafi zamantakewar aure.
Hassana ta bayyana wa kotu cewa ta auri Abdullahi shekaru 30 da suka wuce sannan su na da ‘ya’ya shida tare.
Ta ce ta gaji da zama da Abdullahi saboda yadda ya maida giya ruwan sahn sa. Sannan idan ya sha wannan giya ya dawo gida babu abinda yake yi illa jibgan ta kawai.
” Bayan haka Abdullahi baya salla sau biyar a rana kamar yadda sauran musulmai ke yi sannan ko da ake azumin watan Ramadan Abdullahi bai yi dauki ko daya ba.”
Hassana ta ce a dalilin haka ne take rokon kotu da ta raba auren su domin ta gaji da zama tare da shi haka nan.
Shi kuwa Abullahi bai musanta korafin da matarsa tayi akan sa ba sai dai ya roki kotu da kada ta raba auren su domin har yanzu yana son matar sa.
Abdullahi wanda ma’aikacin shara ne a Efab Estate dake Dutse Abuja ya dauki alkawarin raba albashin sa biyu a rika ba matar sa rabin albashin.
” Daga yanzu na tuba bazan sake shan giya ba balle na duke ta sannan zan yi kokarin bin hukunce hukuncen addinin musulunci.
A karshe alkalin kotun Abdulwahab Mohammed ya daga ci gaba da shari’ar zuwa ranar 28 ga watan Yuni sannan ya umurci Hassana da ta sa wa Abdullahi ido saboda a sami tabbacin ingancin tubar sa.