KATSALANDAN A KASAFIN 2018: Buhari da Majalisar Tarayya sun nuna juna da tsinin mashi

0

A yau Laraba ne Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a kan Kasafin 2018, watanni shida bayan da ya gabatar da kasafin a gaban Majalisar Tarayya.

Da ya ke sa hannu inda nan take kasafin ya zama doka, Buhari ya nuna damuwa da kuma zargin irin yadda Majalisar Tarayya da ta Dattawa suka yi wa kasafin katsalandan din da ake kira aringizo, ko kuma zure.

Buhari ya ce, abin damuwa dangane da kasafin shi ne yadda Majalisa ta yi masa katsalandan, ta hanyar cusa wasu ayyukan da kusan zai ce da wahalar gaske a iya gudanar da su a cikin kasafin.

Sai dai kuma jim kadan bayan kammala wannan jawabi na sa, Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dattawa, Sanata Bala Na’Allah ya wakilci Shugaban Majalisar Dattawa ya maida martani.

Shi ma Hon. Alasan Ado Doguwa, wanda shi ne Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Tarayya, ya wakilci Kakakin Majalisa Yakubu Dogara ya maida wa Buhari raddi.

Bala Na’Allah ya ce ai dama bai yiwuwa haka kawai daga Shugaba Buhari ya turo musu kasafi kawai sai su sa masa hannu ba tare da yin wani bin-kwakkwafi ba.

Ya ce a yadda Buhari ya damka musu kasafin, da a ce sun yi azarbabin sa masa hannu har suka maida da wuri, to da za su kwashi ‘yan kallo su da wadanda suka zabe su domin su wakilce su.

Ya kara da cewa sun fahimci dole su yi wa kasafin katsalandan saboda sun lura an fi karkata ayyukan raya kasa a wasu shiyyoyin kasar nan, yayin da aka bar wasu shiyyoin babu wasu ayyukan a zo a gani har a yaba da aka ware za a yi musu.

Hon. Ado Doguwa kuwa cewa ya yi, ai dama aikin su kenan su duba kasafi su yi gyare-gyare ba kawai su zama ‘yan amshin-Shata su sa masa hannu ba tare da sun tsetstsefe shi ba.

Ya ce da ba su da muhimmanci a cikin batun kasafin kudi, ai da doka ba ta ce a rika kawo musu su duba ba.

Wannan dubawa da suke yi kuwa inji Doguwa, ba wai su kalla kawai su sa hannu ba ne. Ya ce sai sun yi nazari su ga wane bangare ne aka danne a wajen ware wa kaso mafi kankantar yi wa aiki ko ayyuka a cikin kasafin?

Wannan ne ya ce suke dubawa su yi gyare-gyare.

Na’Allah ya kara da cewa Buhari na da damar da zai yi magana kan gyare-gyaren da muka yi, amma dai abu mafi muhummanci shi ne a yau kasafin nan ya zama doka. Don haka sai ya jajirce a yi amfani da shi kamar yadda ya dace.

Share.

game da Author