Gambo Jimeta na nan da ran sa

0

Kamar yadda aka ruwaito a kafafen yada labarai cewa Allah yayi wa tsohon shugaban ‘yan sanda Gambo Jimeta rasuwa, ‘Yan uwan sa sun sanar mana cewa ba haka bane wannan magana. Shi Gambo na nan da ran sa bai rasu ba.

Ko da yake wani dan uwan sa ne ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa ya rasu, sai dai ashe shima kuskure yayi bayan mun sami tabbacin yana raye daga ‘ya’yan sa na cikin sa.

Mu na neman afuwa ga iyalan sa da masu karanta mu cewa in Allah ya yadda irin haka ba zai sake faruwa ba.

Share.

game da Author