Matakai 9 da gwamnati za ta bi don kauce wa sake barkewar rikicin Fulani da Manoma har abada

0

Gwamnatin Tarayya ta fito da wasu matakai da ta ce idan ta aiwatar da su, za a kauce wa sake barkewar rikici tsakanin Fulani makiyaya da kuma manona har abada a kasar nan.

Mashawarcin Tsare-tsaren Ayyuka ga Majalisar Tattalin Arziki ta Kasa, Andrew Kwasari ne ya bayyana haka, a lokacin da ya ke mika daftarin matakan ga majalisar jiya Talata a Abuja.

Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ne Shugaban Majalisar. An gabatar da daftarin a gaban Ministan Gona Audu Ogbe da Gwamnan Benue Samuel Ortom.

1 – Akwai shirin inganta tattali arziki: Shi wannan shiri zai fi bada karfi ne wajen samarwa ko inganta wuraren kiwo domin amfani da haka don inganta tattalin arzikin kasa.

2 – Shirin sasanta rikice-rikice da rashin jituwa a tsakanin juna: Wannan kuma gwamnati ta ce za ta kara inganta tsarin gina al’umma ta yadda za a kara samun yarda da aminta juna a zamantakewar tare a wuri dya

3 – Shirin tabbatar da bin doka da oda: Karkashin wannan shiri za a rika wayar da mutane kai kan illar karya doka da kuma sakamakon hukuncin da zai biyo baya, wato kashe-kashe da kone-konen lalata dukiya. Sannan za a wayar wa mutane kai kan cewa doka za ta rika hukunta wadanda aka kama da laifi.

4 – Shirin bayar da kayan agaji ga wadanda rikice-rikice suka ritsa da su: A karkashin wannan shiri, gwamnati za ta sake gina matsugunai da gidaje, masallatai, coci-coci da rumfunan kasuwannin da aka lalata sakamakon rikicin makiyaya da Fulani.

5 – Sai shirin wayar da kai da samar da Ilimi da kuma isar da sakonni.

6 – An ware jihohi goma da za a fi maida hankali wajen wannan shiri, da suka hada da: Adamawa, Benue, Ebonyi, Edo, Kaduna, Nassarawa, Oyo, Plateau, Taraba da Zamfara.

7 – Za kuma a gina kananan wuraren kiwon dabbobi da za su dauki shanu daga 30 zuwa 100 sai kuma manyan wuraren kiwo da za su iya daukar shanu 1000.

8 – An tsara wuraren kiwon yadda za su fi karkata wajen haihuwa da samar da nama da kuma madara mai tarin yawa.

9 – Gwamna Ortom ya ce baya ga wannan kokari da gwmnati ke yi, to ya kamata ta tabbatar da cewa an kamo dukkan masu hannu a wannan kashe-kashe an hukunta su.

Share.

game da Author