Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a kasafin kudin 2018

0

A yau Laraba ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a kasafin kudin 2018.

Mai ba shugaban kasa shawara kan harkar majalisar dattawa Ita Enang ne ya kai wa shugaban kasa kasafin kudin daga majalisar kasa.

Sai dai kuma a wannan karon da shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da na wakilai, Yakubu Dogara duk basu halarci saka hannun ba.

Mataimakin shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa ne Sanata Bala Ibn Na’Allah ya raka kasafin a wannan karo.

Share.

game da Author