Majalisar Dinkin Duniya ta yi horo ga Najeriya a rika kare ‘yan mata da kananan yara, wadanda Boko Haram suka maida matayen su da karfi da yaji, suka ci mutuncin su.
Wakiliyar Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya a Al’amurran Kula da Wadanda aka ci wa Zarafi a Dalilin Rikice-rikice, Pramila Patten ce ta bayyana haka a wani jawabin ta a ranar tunawa da Kawar da Tirsasa Lalata da Mata da Cin Zarafin su ta Duniya.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, ya ruwaito cewa ‘an mata su na fuskantar wata irin tsangwama da kuma cin zarafin yin lalata da su da Boko Haram ke yi ba tare da amincewar su ba.
Ta ce kamata ya yi al’umma su taru su nuna musu kauna da goyon bayan fitar da su daga halin kuncin da Boko Haram suka jefa su, maimakon a rika tsangwamar su.
A wurin taro an nuna wani dan karamin bidiyo mai suna “Khadija’’, wadda labarin da ke ciki ya nuna Boko Haram sun sace kuma sun gudu da ita, suka maida ta matar su, kuma har ta haifi da a hannun su bayan sun dirka mata ciki.
Patten ta tuna wa masu sauraro haduwar da ta yi da wasu ‘yan mata da Boko Haram suka yi wa ciki suka haihu, wadanda ta ce ta hadu da su a Maiduguri, babban birnin jihar Barno, a cikin 2017.
“Na hadu da ‘yan mata 200, wadanda na samu da jinjirai 162. Abin ya bakanta min rai matuka, ganin yadda su wadannan ‘yan mata da ma yaran da suka haifa, duk iyayen su sun yi watsi da su, su na kyamatar su da tsangwamar su.
“Abin haushi da tausayi da takaici, wai a cikin sansanin ‘yan gudun hijira ma tsangwamar irin wadannan ‘yan mata da ‘ya’yan su ake yi.”
Daga nan ta yi kira da a rika kulawa da su, maimakon a rika tsangwamar su, domin tilasta musu daukar ciki aka yi, bayan an sace su.
Ta ce wannan kawai ma ba karamin abin bakin ciki ba ne ga su ‘yan matan.
Discussion about this post