GOGUWAR ISKA: Buhari ya jajinta wa mutanen jihar Bauchi

0

Fadar shugaban kasa ta jajinta wa mutanen jihar Bauchi bisa ga Ibtila’in goguwar iskar ruwan sama da ya fadawa mutanen jihar inda akalla mutane takwas suka rasu a dalilin haka.

Kakakin shugaban kasa, Garba Shehu ya sanar da haka a yau Talata.

Shehu yace goguwar ta rusa gidaje 1505 a cikin babbar birnin jihar Bauchi sannan mutane 120 sun sami rauni duk a sanadiyyar wannan goguwa.

Bayan haka Shehu ya kuma bayyana cewa anyi gobara a kasuwar garin Azare inda kasuwar da wasu gidaje suka kone kurmus.

A dalilin haka shugaba Buhari ya aika wakilan sa tare da shugaban hukumar bada agajin gaggawa (NEMA) Mustapha Maihajja su ziyarci jihar domin ganin yadda gwamnati zata taimakawa mutanen da abin ya shafa.

Share.

game da Author