Kasar Amurka za ta tallafa wa Najeriya da dala miliyan 102

0

Jakadan kasar Amurka a Najeriya Stuart Symington ya bayyana cewa kasar Amurka za ta tallafa wa mutanen da ke fama da matsalolin rike-rikice a yankunan su da dala miliyan 102.

Symington ya ce kasar ta amince ta tallafa wa mutanen yankin arewa maso gabashin kasar nan musamman wadanda suka rasa matsugunonin su, abinci, kiwon lafiya da tsaro.

Ya ce Najeriya za ta sami wannan tallafin ne ta ofishin su dake kula da irin wadannan matsaloli kamar su USAID, (FFP), (OFDA) da ‘U.S. State Department’s Bureau for Population, Refugees, and Migration.’

Share.

game da Author