Gobe Laraba Buhari zai sa hannu a kasafin kudi na 2018

0

Fadar Shugaban Kasa ta bayyana cewa gobe Laraba Shugaba Muhammadu Buhari zai sa hannu a kan kasafin kudi na 2018, domin fara aiki da shi.

Kasafin dai dai ba zai zama doka ba, har sai shugaban kasa ya sa masa hannu tukunna.

Wannan bayani ya na cikin wani sakon da Fadar Buhari ta bayyana a shafin ta na tweeter yau Talata.

Sanarwar ta kara da cewa zai sa hannun ne da misalin karfe 12 na rana.

Daga nan kuma sanarwar ta ci gaba da cewa an dage taron mako-mako na wannan satin na Majalisar Zartaswa da Buhari ke shugabanta a kowace Laraba.

Share.

game da Author