Rundunar Sojojin Saman Najeriya sun fara kai wa ‘yan ta’addar jihar Zamfara hari ta hanyar yin amfani da jiragen sama.
An yi haka da tunanin cewa shi ne kadai hanyar da za a iya kawo karshen munanan hare-haren da suke kai wa mutanen karkara su na yi musu kisan-kiyashi.
Kwamandan Sojojin Saman Kai Daukin Gaggawa, Caleb Olayera ne ya yi wannan bayanin a lokacin da ya ke tattaunawa da manema labarai a Gusau.
Ya yi bayanin ne bayan karbar wasu jiragen yaki biyu da ya yi jiya domin kara wa dakarun sa karfi da kuma kayan fama.
Ya ce harin ta sama da aka fara kaiwa, ya na daya daga cikin hare-haren da ake kai wa maharan ta hanyar amfani da sojojin kasa, ‘yan sanda, Civil Defence domin fatattakar maharan gaba daya.
Ya kara da cewa gina filin saukar jirage masu saukar ungulu da aka yi a jihar Zamfara an yi ne domin saukar jiragen da ake kai hare-hare kan ‘yan ta’addar jihar Zamfara.