Sanata Ahmed Makarfi ba boyayye suna bane a siaysar Najeriya musamman a ‘yan Shekaru baya da suka gabata.
A jihar Kaduna kuwa, Limamin raya birane da karkara kamar yadda mutanen jihar suka yi masa lakabi da ya taka rawar gani matuka wajen samar da zaman lafiya da raya jihar da ayyukan ci gaba a lokacin da yake gwamnan jihar a tsakanin 1999-2007.
A baya bayan nan kuwa shine ya jagoranci jam’iyyar PDP bayan rikici ya turnike jam’iyyar an rasa gaba an rasa baya, ya daura kambun sa na iya sulhun ta mutane ya ceto jam’iyyar daga durkushewa inda har Allah yasa tayi zaben shugabannin ta lafiya lumui sumul.
A yanzu ma dai wata badakalar ce za a sake shiga idan har ba ayi kaffa-kaffa ba domin zuwa yanzu, akwai tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da tuni ya fito da yunwar sa a fili na neman takarar shugabancin Najeria a inuwar jam’iyyar PDP din, Akwai tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido shima ya fito sannan yanzu kuma da Makarfi ya fito takarar shima.
Alamu dai sun nuna tun a wancan lokacin cewa jam’iyyar PDP da manyan jiga-jigan ta sun fi karkata da Ahmed Makarfi saboda sun fi ganin jajurcewar sa ga jam’iyyar fiye da kowa. Cikin wasu daga cikin dalilan da ya sa suka ga shine kawai mafita ga jam’iyyar ya hada da rashin wani laifi da hukumar EFCC ke bibiyar sa dashi, sannan kuma akwai yarda da dattaku a cike da shi.
Masu yin fashin baki a siyasar Najeriya sun yarda cewa Idan dai har jam’iyyar PDP tana so ta taka rawar gani a zaben 2019, dole sai sun fidda dan takara da zai iya gogawa da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari musamman a Arewacin Najeriya.
ATIKU ABUBAKAR
Eh, lallai Atiku Abubakar dadadden suna ne a siyasar Najeriya, kuma fitaccen dan siyasa ne sai dai ana ganin tasirin sa a Arewa ba zai kai yadda ake bukata ba da zai goge raini da shugaba Muhammadu Buhari ba.
Duk da hamshakin attajirine, wasu da dama na ganin farin jinin sa a yankin arewa akwai tambaya.
Da yawa na ganin mulkinne kawai a gaban sa ba wai ci gaban kasa Najeriya ba sannan shekarun sa sun yi nesa da yawa domin a yanzu haka Atiku na da shekaru sama da 70 ne a duniya.
‘Yan siyasa na tsoro saboda gogewar sa zai iya zama musu matsala ta inda maimakon su iya shanawa sai shine kadai zai shana a siyasan ce.
SULE LAMIDO
Shi ko Sule Lamido, ba a dauke shi da gaske ya keyi ba a wurare da yawa, musamman ganin yadda yake a dumulmule cikin kamayamayar zargin handame kudaden jihar Jigawa lokacin da yake gwamnan jihar.
Har daure shi anyi a hukumar EFCC na dan kwanaki kafin aka ba da belin sa da ‘ya’yansa bisa zargin waske wa da biliyoyin nairori na jihar Jigawa.
Jam’iyyar ba za tayi wa kanta adalci ba idan har tace shi ne za ta ba takarar shugaban kasa a 2019.
Duk da cewa ya goge a harkar siyasa, sunan sa ba zai yi tasiri ba a musamman yankunan kudu na Najeriya.
Ko da yake ba a san ko su waye sauran ‘yan takaran da zasu fito ba, a yanzu dai ‘yan jam’iyyar sun fi ganin shi Makarfi ya fi zama wadda kila ya iya tabuka abin azo a gani idan ya zamo dan takarar shugabancin Najeriya a Inuwar Jam’iyyar PDP din.
FARIN JININ BUHARI
Kila wasu da yawa za su ce goguwar Buhari ta zama iska yanzu. Domin Kuwa kusan mutane da yawa na ganin irin burin da suka yi wa mulkin musamman a Arewacin Najeriya abin kamar da wuya. Ada ko ina ka bi zaka ji ana sai Buhari amma yanzu abin ya dan yi kasa-kasa.
Hakan nuni ne cewa lallai akwai gajeruwar matsala ko a yankin arewa da ake ganin nan ne Buhari yake da dandazon magoya baya.
Sai dai kuma duk da hakan mutane na ganin shi Buhari ma ba sai yayi abin da ake so ba, soyayyar sa a zukatan mutane baya taba gushewa.
An dan sami baraka a jam’iyyar APC matuka inda kusan duk wadanda suke tare da shugaban kasar a wasu lokutta sun nuna rashin jin dadin su kan yadda yake gudanar da mulki a kasar nan.
Idan ba a manta ba, gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya yai wa shugaba Buhari shimfidaddiyar wasika inda ya koka kan yadda yake gudanar da mulki a tun farkon fara wannan mulki, haka ita kanta mai dakin shugaba Buhari, Aisha Buhari, ta yi irin wannan korafi inda har tayi barazanar kin mara masa baya idan ya fito takara a 2019.
Ko da yake kila wadannan maganganu da suka yi ya canza yanzu, duk da haka dai akwai sauran rina a kaba.
Fito da mutane irin su Makarfi a wannan lokaci zai iya yi wa jam’iyyar adawa ta PDP tasiri domin kuwa komai karancin kuri’un da za su samu a arewa zai yi matukar tasiri a zaben wajen tada wa APC da shugaba Muhammadu Buhari hankali, ganin cewa har yanzu yankin kudu maso gabas, da kudu mao kudu basu yin APC kwata-kwata. Ga kuma illar da hasalallun ‘yan sabuwar PDP da suna nan suna hura hanci amma kuma ba su fice daga APC ba.
Kila karrama marigayi Abiola yayi wa jam’iyyar tasiri a yankin Kudu Maso Yamma.
Ga fili ga doki.