Shigo da matasa cikin gwamnati yafi tabbatar da kudirin rage shekarun yin takara, Daga Mustapha Soron Dinki

0

Yau a Najeriya koda za’a mayar da shekara ashirin a matsayin shekarun yin takarar Gwauna ko sanata matasan da zasu iya tsayawa takarar basu da yawa duba da matsanancin hali da suke ciki na talauci da rashin aikin yi.

Domin matasa masu shekara talatin ma basu da yawa da zaka samu suna da harafin A da yawa a cikin rayuwarsu sai dai B. Idan nace ‘A’ ina nufin “Akwai” Shi kuma harafin ‘B’ yana nufin “Babu” Saboda mafi yawancinsu zaka samesu babu aikin yi,babu mata,babu gida,babu ko keken hawa sannan kuma babu kulawar al’umma akansu.Kunga ko a nan na lisaffa babu guda biyar.To mutumin da yake cikin wannan yanayin ne zai iya takara,shi takararsa ma abunda zai kai bakinsa.

Tun ran gini tun ran zane, bazai yiwu ba ace mutumin da yake da shekara talatin ace an sameshi a aji biyu na jami’a kuma ace wai an rage masa shekarun tsayawa takara in dai ba sakacinsa bane yasa bai koma makaranta da wuri ba.Bashi da bukatar a rage shekarun tunda dama shi ya riga ya kai ma.

Matasan Najeriya suna fama da matsaloli ne goma-da-goma. Na farko shi kansa tsarin ilimin kasar bai yi daidai da duniyar yau ba.Na biyu,dole ne sai anyi juyin juya hali a kasuwar aikin yi ta Najeriya,wadannan masu son rai da suke bawa zuri’arsu aiki da kuma masu siyar dashi a gari sai an dauki mataki akansu. Sannan dole sai gwaunati ta dinga saka matasa a cikin mukamanta na siyasa don su koyi mulki da gudanarawa.

Ku fahimceni,ba ina cewa sai tsofaffin Najeriya sun daina mulki ba. Abun nufi a nan shine,dole ne sai an dinga ware wani kaso na ‘Appointment’ din gwamnati ana bawa matasa don a dama dasu ko kuma a basu aikin yi wanda zai basu damar tara kudin komawa siyasa. Ta wannan hanyar ne zasu koyi aikin a wajen wadanda suke rike da kasar yanzu. Kamar dai misalin ‘Attachment’ da ake tura dalibi don ya samu kwarewa saboda a samu kyakykyawar yanayi na siyaysa.

Amma rashin yin hakan zai sa Najeriya ta dinga iyo a waje daya. Idan muka kalli matasan da suke mulkar kasashen duniya yanzu mafi yawanci ta haka suka fara.Wani ma zaka ga ya riqe muqamin bawa shugaban da ya gada shawara kamar Saleh Ali na Yemen. Emannuel Macron na France shima saida ya gama aikin bakinsa sannan ya zama shugaban kasa.Amma rage shekarun takara ba shine ba,aikin yi ta hanyar bayar da sana’a ko muqami ne kawai zai bawa matasa damar shigowa siyasar Najeriya don siyasa da talauci basa jituwa.

A matsayina na matashi dan Najeriya wawalidin Wamawalad.Ta uwa da uba ni dan kasa ne.Bani da wata kasa kamar ita don haka ya zama dole a kaina na haskawa gwamnati hanya saboda a shawo kan matsalar. Na rantse da Allah matasan kasar mu basu da buri sosai idan ka hada da matasan kasashen Afrika.Yanzu kaga muna cewa munfi Nijar da Benin arziki ko,to idan har ‘yan wadannan kasashe suna samun kudi sun fi namu almubazzaranci. Basu da kan-gado wajen kashe kudi. Amma mu kalli shirin Npower da Buhari ya kawo yadda wasu suka samu nutsuwa da dubu talatin din da ake basu a wata.A ganin wasu ma don ta kare ayi gobara.Ko yanzu akace musu kule zasu cewa aure cas.

Naga wani Nopwerist ma ya bugo fasta zai yi takara. Wannan shi zai nuna maka cewa akwai bukatar a samawa matasan nan abun yi kodai wata hirfa da zasu dinga samun kudi shine zakaji amonsu a gari sun fito takara.

Allah ya shiryar damu.

Share.

game da Author