Hukumar Alhazai ta Najeriya ta tabbatar da cewa ta na nan ta na tsare-tsaren inganta matakan kula da lafiyar mahajjatan Najeriya a kasar Saudi Arebiya yayin aikin Hajji na 2018.
Dangane da wannan ne Hukumar ta shaida cewa ta kafa tawagar jami’an kula da lafiyar mahajjata daga jami’an kiwon lafiya na fadin jihohin kasar nan baki daya, har da Abuja.
Shugaban tawagar masu kula da lafiyar mahajjata, Ibrahim Kana, ne ya shaida wa PREMIUM TIMES haka, dangane da irin shirye-shiryen da ke gudana.
Ya kara da cewa an gudanar da aikin wayar wa maniyyata kai tare da ba su horo da aka kammala makonni biyu da suka gabata.
“Su ma jami’an kula da lafiyar mahajjata din an ba su horo da sanin makamar aikin lafiya kan wasu cututtuka da suka shafi batun cutar zazzabin Lassa da kuma hanyoyin kauce wa kamuwa da kuma magance su.”
Ya kara da cewa an rigaya an ware dukkan alluran rigakafin da ake bukata a yayin wannan aikin Hajji mai zuwa na 2018.