Najeriya ta kwashi kashinta a hannun Croatia

0

‘Yan wasan kwallon kafar Najeriya ‘Super Eagles’ sun kwashi kashin su a hannun su, bayan zane su da kasar Croatia ta yi a wasan cin kofin duniya da ake bugawa a kasar Rasha.

Najeriya dai bata buga wani abin azo a gani ba a iya tsawon awa daya da rabi da akayi ana doka tamolar.

A tsanaki kasar Croatia ta jefa kwallayenta biyu ba tare da Najeriya ta iya maida ko da kwallo daya bane.

Kafin wanna wasa, kasar Argentina da suke rukuni daya da Najeriya ta buga kunnen doki da kasar Iceland duka da cewa shahararren dan wasan duniyan nan Leo Messi ya kasa jefa kwallo da ga kai sai gola.

Kasar Faransa ta doke Australia da ci 2-1, Peru sun sha Kashi a hannun Denmark da ci daya mai ban haushi.

Share.

game da Author