Ku taya Buhari da addu’a, makiya na son su ga bayan sa – Gwamna Ganduje

0

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya roki wadanda yayi wa yafiya, wato ‘yan fursunan da gwamnati tayi wa yafiya da su taya shugaban kasa Muhammadu Buhari da addu’a Allah ya kare shi daga hassadar makiya.

Ganduje ya ce shugaba Buhari na bukatar irin wannan addu’oi daga kowa da kowa, har da suma ana bukatar irin wanna addu’oi daga garesu.

” Roko na gareku shine yadda muka sama muku ‘yan cin kai wato muka sallame ku yau, abin da muke rokon ku da shi shine ku taya shugaba Buhari da addu’o’i domin samun nasara kan masu shirya masa nukufurci, makininita, gutunguila da bita da kulli a kasar nan.

” Buhari ya umarci gwamnonin kasar nan da su rage yawan cinkoso a gidajen yarin kasar nan. Dalilin haka ne yasa mukayi haka a gareku.

Gwamna Ganduje ya yi wa fursinoni sama da 300 yafiya da ke gidajen yaji dabam dabam a fadin jihar.

Share.

game da Author