Baki da baki na gayawa Sule Lamido ba zan zabe shi ba – Orji Kalu

0

Tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Kalu ya bayyana wa gwamnan jihar Jigawa Badaru Abubakar cewa duk da abokantakar dake tsakanin sa da Sule Lamido ba zai zabe sa ba a 2019.

” Na gaya wa Sule kuru-kuru cewa ni dai ba zan yi shi ba domin kuwa Buhari ne zabi na.

” Kuma dai kowa ya sani tsohon gwamnan Jigawa Lamido amini nane amma Buhari ya sha gaban sa a wannan karon. Ba zan iya yin kowa ba idan ba shi ba.

Kalu ya kara da cewa ya fara zagayen nema wa Buhari kuri’u ne inda ya fara yada zango a garin Dutse, babban birnin Jigawa.

Share.

game da Author