Shugaban hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko na jihar Neja (SPHCDA) Yahaya Na’uzo ya bayyana cewa mutane shida sun rasa rayukansu sanadiyyar kamuwa da cutar amai da gudawa a jihar.
Na’uzo ya bayyana haka ne ranar Alhamis a lokacin da yake ganawa da Kamfanin dillancin Labaran Najeriya a Minna.
Ya ce mutane 43 ne suka kamu da cutar a kananan hukumomin Bida,Gbako da Katcha sannan daga cikin ne mutane shida suka rasa rayukansu.
” Muna kira ga duk mazauna karkara da su rika tsaftace muhallin su musamman ruwan shansu ganin cewa duk wadanda suka kamu da cutar duk daga rashin amfani ne da ruwa mai kyau ya jawo musu wannan cuta.
” Sannan a duk lokacin da kaji jikin ka ba ya maka dadi hanzarta zuwa asibiti maza- maza.
A karshe ya ce hukumar su za ta ci gaba da wayar wa mutane kai musamman mazauna karkara don sanin muhimmancin tsaftace muhalli da hanyoyin gujewa kamuwa da cutar.