ADAMAWA: Kotu ta ce a biya malaman firamare da aka kora albashin su na watanni 29

0

Kotun dake sauraren kararrakin ma’aikata ta umarci gwamnatin jihar Adamawa ta biya malaman makarantar firamari sama da 600 da ta kore tun a farkon 2015.

A farkon 2015, gwamnatin jihar Adamawa ta sallami malaman firamari sama da 600.

Kotun ta ce har zuwa lokacin da take yanke wannan hukunci, gwamnatin jihar bata kawo shaidun da ya nuna tabbacin sallaman wadannan malamai wanda hakan ya sa kotun ta yanke hukuncin har yanzu malamai ne a jihar.

A yadda hukuncin ta kaya, yanzu dole jihar ta yi aman sama da naira miliyan 600 ta biya wadannan malamai da ta kora ba a kan ka’ida ba.

Lauyan malaman, Abubakar Babakano ya jinjina wa kotun kan wannan hukunci da ta yanke, yana mai cewa wannan hukunci nuni na cewa ba ayi wa malaman adalci ba.

Wadannan malamai na firamare dai an dauke sua aiki ne tun a mulkin tsohan gwamnan jihar, Murtala Nyako.

Share.

game da Author