Jami’an tsaro sun kama ‘yan sara suka 50 a Kaduna

0

Kakakin gwamnan jihar Kaduna Samuel Aruwan ya bayyana cewa jami’an tsaro sun kama ‘yan sara suka 50 a cikin garin Kaduna.

” Gwamnan jihar Kaduna ya sami labarin cewa ‘yan sara suka na neman tada zaune tsaye a jihar wanda hakan ya sa ya umurci jami’an tsaro a jihar su tabbata sun kamo duk wani marakunyar yaro dake neman tada hankalin jama’a a jihar.

Unguwannin da suka fi fama da wannan masifa na yara ‘yan sara suka sun hada da Tudun-Wada, Kawo, Badarawa, Unguwan Sanusi da sauran su.

Aruwan yace bisa ga umurnin gwamna El-Rufai jami’an tsaro da ma’aikatar shari’a za su gurfanar da wadannan matasa a kotu bayan sun kammala gudanar da bincike a kan su.

A karshe Aruwan ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar Kaduna baza ta amince da duk wani kungiyar ‘yan banga ba idan ba kungiyar ‘yan bangan da ta kafa ba sannan ta amince da su ba.

Sannan idan ana bukatan a taimaka a fannin tsaro na jihar za a iya aikawa da sunayen wadanda ake so su zama ‘yan bangan ga jami’an tsaron jihar domin tanttance su.

Ya ce hakan zai taimaka wa jihar wurin guje wa yin amfani da ‘yan ta’adda a matsayin masu samar da tsaro a jihar.

Share.

game da Author