Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara Muhammad Shehu ya bayyana cewa mutane 10 sun rasa rayukansu sanadiyyar harin da wasu mahara suka kai a kauyuka biyu dake karamar hukumar Birnin-Magaji.
Shehu ya bayyana cewa wannan abu ya faru ne a daren Talata da karfe 10 a kauyukan Dutsen –Wake da Oho.
” Bayan an sanar da mu abin dake faruwa sai muka gaggauta zuwa karamar hukumar Birnin – Magaji amma a lokacin da muka isa wurin sai muka tadda maharan sun riga sun tsere, shiga dajin Rugu dake iyakar jihohin Katsina da Zamfara’’.
Ya ce sun tsinto gawar mutane bakwai a kauyen Dutsen –Wake sannan uku a kauyen Oho.
A karshe shehu ya ce rundunar su za ta hada gwiwa da rundunar ‘yan sandan jihar Katsina domin kama wadannan mahara sannan ya yi kira ga mutanen karamar hukumar da taimaka wa jami’an tsaron da duk wani bayanan da suka sani zai taimaka wurin kama wadannan muggan mutane.
Discussion about this post