A ranar Talata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Anas Sabir sabon shugaban asibitin koyarwa na jami’ar Usman Danfodiyo (UDUTH) dake jihar Sokoto.
Jami’in asibitin Buhari Abubakar ya sanar da haka a Sokoto.
Ya ce sun sami tabbacin haka ne daga wasikar da shugaba Buhari ya rubuto ta hannun mininstan kiwon lafiya Isaac Adewole.
A wasikar Buhari ya hori Sabir da ya yi amfani da wannan dama domin samar da sauya-sauye na ci gaba da zai inganta kiwon lafiya a jihar.
Sabir ya maya gurbin Yakubu Ahmed.
Discussion about this post