KILU TA JA MASA BAU: Spain ta kori mai horas da ‘yan wasa a jajibirin fara gasar cin kofin duniya

0

Ruwan-idon da mai horas da ‘yan wasan kwallon kafa na kasar Spain, Julen Lopetegui ya nuna, ya janyo masa kora daga kungiyar, kwanaki biyu kafin fara gasar cin Kofin Duniya da za a fara fafatawa ranar Juma’a a kasar Rasha.

Lopetegui, wanda kwanan nan ya sa hannun amincewa da ci gaba da horas da ‘yan wasan Spain har tsawon shekaru biyu zuwa bayan kammala gasar kofin Turai a 2020, ba zato ba tsammani kuma sai aka ji ya sa hannun amincewa da horas da ‘yan wasan Real Madrid da ke Spain, a kwantaragin shekaru uku.

An kori Lopetegui kwana biyu kafin Spain ta kara a wasan ta na farko da Portugal, wadda ke rike da kambun kofin kasashen Turai.

Ronaldo na daya daga cikin ‘yan wasan Portugal, wanda tuni dan wasan Barcelona, Andres Iniesta da ya bar kulob din kwanan nan, ya gargadi Spain da cewa idan su na son su gama lafiya, to sai sun hana Ronaldo yin rawar gaban hantsi a cikin filin kwallo.

A jiya ne dai Real Madrid ta yi sanarwar cewa ta dauki kocin na kasar Spain aiki, amma sai bayan an kammala gasar cin kofin duniya da za a fara a Rasha sannan zai fara aiki.

Wannan sanarwa ta bakanta wa Hukumar Kwallon Kafa ta Spain rai, inda ba tare da wata-wata ba, suka kira taron manema labarai na gaggawa can a kasar Rasha, suka sanar da korar sa.

A yanzu dai zai zarce kenan a Real, inda ya sa hannun komawa.

Daukar Lopetegui ya biyo bayan ajiye aikin da Zinedine Zidane ya yi, inda ya tafi koyar da ‘yan wasan kasar Qatar, kasar da za ta dauki nauyin gasar cin kofin duniya a 2022.

Zidane ya sa hannu a kan kwangilar shekara hudu, kan kudi tsababa har fam miliyan 50, kudin da ake ganin babu wani mai horas da ‘yan wasa da aka taba bai wa wadannan kudade.

Wani karin tagomashi da ke tattare da kwangilar Zidane, shi ne yadda gwamnatin kasar ta rattaba cewa ba za a cire masa ko kwandala a matsayin kudin haraji daga cikin albashi da alawus din sa ba har tsawonn shekara hudu.

Sai dai ana sa ran bayan kammala horaswar sa ta shekaru hudu a Qatar, Zidane zai koma ya ci gaba a Real Madrid, ganin yadda ba a so tafiyar sa ba, kuma ya jaddada cewa nan ba da dadewa ba zai iya komawa kulob din.

Kafin ya fara koyar da Spain, Lopetegui ya taba koyar da ‘yan kasa da shekaru 17 da kuma kasa da shekaru 20 na kasar Spain.

Sannan kuma ya taba shafe shekaru uku ya na koyar da ‘yan wasan FC Porto na kasar Portugal.

Tun da ya karbi aikin koyarwa da horas da ‘yan wasan kasar Spain, babu wata kasa da ta taba yin nasara a kan kasar, a wasanni 20 da aka kafsa a karkashin sa.

Spain ta yi nasara sau 14, an yi canjaras da ita sau 6.

Share.

game da Author