Kungiyar matan sojin saman Najeriya za ta horas da mata 150 sana’o’in hannu a jihar Bauchi

0

Shugaban kungiyar matan sojin saman Najeriya na kasa Hafsat Abubakar ta sanar cewa kungiyar su za ata horas da mata a jihar sana’o’in hannu dabam-dabam a jihar.

Hafsat ta bayyana haka ne a taron kungiyar karo na 9 da akayi a garin Azare, jihar Bauchi.

” Wadannan mata za su sami horo ne kan yadda a ke gyaran kai, dinkin kaya, hada sabulu, girki, kwaliya da sauran sun a tsawon makonni 10.”

Malama Abubakar ta kara da cewa kungiyar NAFOWA ta yi haka ne domin ta mara wa gwamnatin tarayya baya kan aiyukkan da take yi na kawar da rashin aikin yi da talauci a kasar nan.

A karshe mai martaba sarkin Katagum Baba Umar-Faruq ya jinjina wa kungiyar NAFOWA kan irin wannan namijin kokari da take yi domin inganta rayukan mutane.

Share.

game da Author