Rundunar ‘Civil Defence’ ta jihar Neja ta taso keyar wani matashi da ta kama da laifin kwarara wa mahaifiyar sa tafasasshen ruwan zafi a jiki.
Jami’in rundunar Philip Ayuba ya sanar da haka wa manema labarai ranar talata a Minna inda ya kara da cewa sanadiyyar hakan mahaifiyar yaron na nan a kwance da konannen jiki.
Ayuba yace wannan yaro ya aikata haka ne a cikin gidan su dake titin Okada dake Minna sannan rikakken mashayin miyagun kwayoyine da giya.
” Muna tsammanin wannan yaro ya aikata haka ne cikin maye. Sannan wannan ba shine karo na farko ba da ya yi kokarin kashe mahaifiyar ta sa ba domin akwai ranar da ya kwada wa mahaifiyar sa lafcecen dutse a kai sannan ya chaka mata wuka domi ya kashe ta amma Allah ya sa ran ta na gaba.”
A karshe Ayuba yace za su kai yaron kotu bayan sun kammala bincike a kan al’amarin.