‘Yan banga sun fatattaki Boko Haram a kauyen Adamawa

0

Kwamishinan yada labaran jihar Adamawa Ahmed Sajoh ya sanar cewa wasu ‘yan Boko Haram sun kai wa kauyen Kaya dake karamar hukumar Madagali hari inda suka kona gidaje 13.

Sajoh ya bayyyana cewa wannan abu ya faru ne ranar Litini da daddare.

Ya ce mafarautan kauyen, ‘yan banga da jami’an tsaro ne sun fatattaki ‘yan Boko Haram din duk da cewa sun kona gidaje 13 a wannan kauye.

” Jami’an tsaron sun sami nasarar kashe daya daga cikin ‘yan Boko Haram din sannan daya daga cikin ‘yan banga ya sami rauni.”

Ya ce yana jinjina wa hada karfi da karfe da ‘yan banga, mafarauta da jami’an tsaro suka yi da har Allah ya basu sa’ar fatattakar ‘yan Boko Haram din.

A karshe Sajoh ya yi kira ga mutane da su ci gaba da zama masu kiyaye doka sannan su ba jami’an tsaro hadin kai musamman yanzu da ake shin yin bukukuwan Sallah a ko ina afadin jihar da duniya baki daya.

Share.

game da Author