KWALARA: Cikin wata daya jihar Adamawa ta rasa mutane 20

0

Jami’in yada labarai na ma’aikatar kiwon lafiyar jihar Adamawa Mohammed Abubakar ya bayyana cewa mutane 19 sun kamuwa da cutar kwalara a jihar.

Ya sanar da haka ne ranar Litini a garin Yola.

Idan ba mata ba a watan da ta gabata ne cutar ta bullo a kananan hukumomi biyu da ya hada da Mubi ta Arewa da Mubi ta Kudu.

” A wancan lokacin akalla mutane 526 a Mubi ta Arewa suka kamu da cutar sannan a cikin su mutane 11 suka rasu, a Mubi ta Kudu kuma mutane 693 ne aka sanar sun kamu da cutar sannan inda mutane tara suka rasu.”

” Ba a gama kashe wannan wutan ba sai cutar ta ci gaba da yaduwa zuwa karamar hukumar Hong. A nan ma mutane biya aka gano sun kamu da cutar. Haka kuma a karamar hukumar Maiha, nan ma an tabbatar mutane uku sun kau da cutar.”

A yanzu dai Abubakar ya ce tsakanin wata daya jihar ta rasa mutane 20 a sanadiyyar yaduwar cutar sannan mutane 19 na kwance a babbar asibitin Mubi.

Share.

game da Author