Jami’in yada labarai na gwamnan jihar Kogi Kingsley Fanwo ya bayyana cewa gwamnati ta gine sabbin gidajen kallon kwallon kafa 25, daya a duk kananan hukumomin jihar.
Fansho ya sanar da haka ne a garin sannan kuma ya ce a duk gidan kallon za a samar da tsaron da ya kamata.
Ya ce gwamnati ta ware kudade na musamman domin siyo manyan talabijin,janareto da duk sauran ababen da za a bukata a wurin kallon kwallon kafar.
Ya kuma ce za su horar da mutane domin sanin yadda za su iya aiki da wadannan na’urorin da za a siyo, za kuma a samar da man fetir isasshe wa janaretocin da za a yi amfani da su sannan da tsaro na musamman.
Najeriya za ata buga wasan ta na farko da kasar Crotia ne ranar Asabar mai zuwa.
Discussion about this post