Hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko na jihar Jigawa ta yi shelar cewa za ta yi wa yara ‘yan kasa da shekara biyar allurar rigakafin cutar shan inna a jihar.
Shugaban hukumar Kabiru Ibrahim wanda ya sanar da haka ya bayyana cewa za su yi wa yara miliyan 1.6 ne allurar a kananan hukumomi 27 dake jihar.
Ibrahim ya kuma ce sun tanadi isassu kuma da kwararrun ma’aikata tare da magungunan alluran daga gwamnatin tarayya domin samun nasaran aikin.