Za a tura zaratan sojojin sama 150 a Taraba

0

Hafsan Hafsoshin Sojojin Sama na Najeriya, Sadiq Abubakar, ya bayyana cewa za a gagguta tura zaratan sojojin sama 150 zuwa domin aikin taimakawa a wanzar da tsaro a jihar Taraba.

Abubakar, ya ce za a tura sojojin saman ne musamman a yankunan da aka fi fama da tashe-tashen hankula.

Ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya jagoranci tawagar manyar hafsashin sojojin sama zuwa kai ziyara wurin Gwamnan Jihar Enugu, Ifeanyi Ugwuanyi a jiya Laraba.

Ya ce a baya sojojin saman sun fi nuna gudanar da ayyukan su ta sama ne, amma a yanzu sun maida hankali ne a kasa.

Sojojin wadanda za a tura a ranar 10 Ga Mayu, 2018, ya ce akwai ma wasu kamar su, su 150 a Dajin Sambisa da ke aiki tare da sojojin kasa.

Abubakar ya ce ya ziyarci jihar ne domin kaddamar da sabuwar hadikwatar horas da sojojin sama a Kudu-maso-Gabas.

Shi ma gwamnan ya yaba da irin rawar da sojojin sama ke bayarwa wajen samar da tsaro da kokarin kakkabe ta’addanci a Najeriya.

Share.

game da Author