YAJIN AIKI: Gwamnati za ta hukunta duk wanda ya muzguna ma wani a wajen aikin sa – Minista Adewole

0

Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya yi kira ga shugabanin asibitoci mallakar gwamnati dake kasar nan da su samar wa likitocin su dake aiki tsaro ta musamman.

Minista Adewole ya yi wannan gargadi ne bayan kukan da kungiyar Likitoci ‘NARD’ ta yi cewa wasu ma’aikatan jinya da ke yajin aiki na yi musu barazana a aikin su.

Adewole ya kuma kara da cewa NARD ta zargi JOHESU da garkama wa dakunan da ake ajiyan kayan aiki na asibitocin kasar nan kwado domin hana mambobin kungiyar gudanar da ayyukan su.

” Yayin da muke tattauna yadda za mu shawo kan wannan yajin aiki muna kira ga JOHESU da ta daina muzgunawa likitoci sannan su guji hana mambobin su da suka ki mara musu baya yin ayyukan su.”

” Tabas kuna da ‘yancin shiga yajin aiki ko zanga-zanga amma dokar kasa bata baku damar rufe ofisoshi ba ko kuma hana wanda yake so ya yi aiki aikin sa ba.”

A karshe minista Adewole ya ce gwamnati ba za tayi kasa-kasa ba wajen ganin gwamnati ta hukunta wanda ya saba wa doka.

Share.

game da Author