Hukumar Kula da Yanayin Sararin Sama ta Kasa (NiMet), ta bayyana cewa a yau Litinin za a sheka ruwan sama a yawancin biranen Najeriya.
NiMet ta ce za a rika jin tsawa mai rugugi a lokacin da ake sheka ruwan a garuruwan Abuja, wani yanki na Kaduna, Benue, Nasarawa, Kogi, Kwara, Plateau, Taraba da Yola.
Hukumar ta kara da cewa kusan ilahirin kudancin kasar nan zai samu ruwan sama a yau Litinin.