‘Yan sanda sun daina maganar satar sandar mulkin Majalisar Dattawa

0

Makonni uku bayan samamen da wasu ‘yan bangar siyasa su ka kai Majalisar Dattawa inda suka arce da Sandar Mulki, har yau ‘yan sandan Najeriya ba su bayar da wani karin haske dangane da bincike da kuma batun ko sun gabatar da wadanda ake zargi a gaban kotu ba.

Rundunar ‘yan sandan ta ki amda kiran da PREMIUM TIMES ta yi mata domin jin halin da ake ciki.

Bayan sace sardar da aka yi aka gudu da ita, washegari ‘yan sanda sun bayyana cewa sun gano ta a karkashin wata gada daidai fita ‘Abuja City Gate’.

Sannan kuma daga baya sun bayyana cewa sun kama mutane shida da ake zargin su da hannu wajen sace sandar mulkin.

Sai dai kuma makonni uku kenan bayan kama mutanen da ake zargin, har yau ‘yan sanda ba su bayar da wani karin haske dangane da batun ba. Kuma babu labarin inda wadanda aka kama din su ke a tsare.

PREMIUM TIMES ta tuntubi kakakin ‘yan sanda Babban Birnin Tarayya, Anjuguri Mamza, wanda ya ce duk wata tambaya dangane da batun, to a tuntubi Hedikwatar ‘Yan sanda ta Kasa.

Share.

game da Author