Tsohon Shugaban Hukumar Zabe Mai Zanta ta Kasa, Attahiru Jega, ya bayyana cewa mambobin Majalisar Tarayya rikakkun kwararru ne wajen neman a ba su cin hanci da rashawa kafin su gudanar da ayyukan da dokar kasa ta wajabta musu su aiwatar.
Da ya ke jawabi a wurin laccar Tunawa da Ranar Dimokradiyya, a Cibiyar Taro ta ‘International Conference Center’ a Abuja, a yau Litinin, ya ji daga bakin da dama daga cikin manyan shugabannin hukumomin gwamnati, sun yi masa korafin yadda mambobin Majalisar Tarayya ke yawan neman a ba su cin hanci kafin su biya wa hukumomi bukatun da doka ta wajabta a biya musu.
Farfesa Jega, ya shaida wa dimbin mahalarta taro, ciki har da Shugaba Muhammdu Buhari, Yakubu Dogara, Babban Alkalin Alkalai na Kasa, Walter Onnoghen cewa “wasu Shugabannin Kwamitocin Majalisar Tarayya basu kware da iya komai ba, sai neman a ba su cin hanci kafin su yi wa hukumomin gwamnatin tarayya abin da ya wajaba su yi musu.”
Wannan bayani da Jega ya yi, ya kara tabbatar da rahoton da PREMIUM TIMES ta yi kwanan baya cewa shugabannin hukumomin gwamnati na koken cewa mambobin majalisar tarayya na uzura musu da neman a ba su toshiyar baki kafin su amince da wata bukata ta su.