‘Yadda sojojin Najeriya da na Kamaru suka rika cin zarafin mata a sansanin gudun jihira’

0

Matan da ke zaune a sansanonin gudun hijira bayan sun kubuta daga Boko Haram, sun bayyana yadda sojojin Najeriya da na Kamaru suka rika cin zarafin su.

Matan sun yi wannan bayani ne a Abuja a wani taro wanda Kungiyar Jinkai ta Duniya, Amnesty International ta shirya, domin gabatar da rahoton ta dangane da abin da ya rika faruwa da wanda ke faruwa a sansanonin gudun hijira.

Wasu kalilan da ga cikin matan sun yi jawabai ga ‘yan jarida a wurin taron.

Wata mai suna Kella Haruna, ta ce ta ga bala’i da rayuwar kunci a sansanin gudun hijira.

Ta ci gaba da cewa sojoji da kuma jami’an tsaron hadin-guiwa sun rika cin mutuncin mata.

Kella wadda ta yi magana cikin harshen Kanuri, ta ce an yi lalata da mata sosai, sannan wasu kuma idan su na so a ba su abinci, to sai sun yarda sun bada kan su an yi lalata da su.

Kella ta ce daga garin Banki ne aka kubutar da su bayan da Boko Haram suka mamaye su.

“Daga nan da aka tura mu cikin Kamaru, mun ga cin zarafi da tozartwa matuka. Domin tsirara suka sa muka yi, haka sojojin kasar suka bar mu kwana hudu babu ko abinci.Haka suka sake maida mu Banki.’’

Kella ta ci gaba da cewa ta tabbatar da mazan su na nan, to babu yadda za a yi su fuskanci cin zarafi da tozartawar da aka yi musu.

“Mu na a Bama ne aka zo aka kama mazajen mu, aka daure musu idanu, aka loda su a cikin mota aka nufi Maiduguri da su. Amma aka ce mana za a kai mu inda mazajen na mu suke, amma kuma har yau din nan babu labari.

“Sojoji suka ce ina matan nan, ku zo za mu kai ku inda mazajen ku suke. Daga nan muka dan tattara komatsan da suka rage mana, muka fito. Suka dauke mu amma duk suka jibge mu a dai cikin Bama din a wani sansanin da ke asibitin garin.

“Maganar gaskiya a sansanin Bama inda nan ne asibitin garin a da, babu maganar abinci, idan ka yi magana kuma su yi ta jibgar ka. Kuma sojoji sun rigaya sun kwace duk kudaden da ke hannun mu. Suka bar mu biyu.”

Daga nan ne kuma inji Kella, sojojin suka fara bibiyar su, wadda suka ga ta yi musu, sai su nemi sai sun yi lalata da ita.

Wata mai suna Fatima Bukar, ta bayyana yadda sojoji suka kame mijin ta, ‘ya’yan ta da ‘yan uwan ta maza.

Ta ce har yau babu wanda ya ce mata ga inda aka tsare su tun da aka kame su aka tafi da su.

“Kafin ma su dauke su daga can su canja musu wuri, sai da suka fito da su, suka yi musu wanka, sannan suka loda su zuwa Maiduguri.’’

Sojoji sun sha cewa wadanda ake kamawa din ana damke su ne domin a bincika a gane shin ‘yan Boko Haram ne ko kuwa ba su ba ne.

Wasu daga cikin wadanda ake kamawa din ana sakin su idan aka gano cewa ba Boko Haram ba ne. Amma kuma da yawa na can a kulle har yau ba a gurfanar da su an yanke musu hukunci ba, su na tsare a hannun sojoji.

YAKAMATA GWAMNATI TA SHIGA LAMARIN

Hamsatu Allamin, wadda ta kafa Allamin Foundation domin dawo da zaman lafiya a Jihar Barno, ita ma ta yi magana a wurin taron inda ta nuna takaicin yadda sojoji da jami;an tsaron na Vigilante suka rika tafka lalata da matan.

“Kai ko ma da soja daya ne tal ko dan CJTF daya ne ya yi wa mace daya fyade, to fa tilas sai an hukunta shi. Duk da cewa yawancin wadannan matan su na tsoron su fito su yi magana saboda tsoron kada wani abu kuma ya biyo baya.

Allamin ta ce an ci zafin mata akalla 1, 600 abin da ya hada har da duka. Ta ce maza akalla mazaje 437 sun bace daga sansanoni

“Ai har gara ma Boko Haram da wasu sojojin. Ba ina magana ne a kan daruruwa ba, sai dai na ce dubbai. Ya kamata a fara ganin canji a fadin kasar nan. Ina fatan hukumar sojoji ba za ta ji haushin wannan ba. Amma ta nemo hanyar magance wannan matsala.

Daraktan Kare Hakkin Wanda aka Zalunta a Hukumar Kara ‘Yancin Dan Adam, ya tabbatar wa Premium Times cewa sun karbi koke-koken cewa akwai mazaje 437 da har yau ba a san inda suke ba.

“Na rubuta wa sojoji takarda, amma sun maido min cewa babu ko daya daga cikin jerin sunayen wadanda ake nema din da ke tsare a hannun su a jihar Barno.

Ita kuwa Sa’adatu Mahdi, daya daga cikin wadda aka kafa ‘Bring Back Our Girls da ita, cewa ta yi bala’in da ake fama da shi a yankin Arewa maso gabas, ya wuce tunanin kowane bil Adama.

“Ai lokacin da aka kama daliban Dapchi, mun rika tuntubar Boko Haram da ba su dauke da makamai, su kuma su na tuntubar fitinannun na su. Da aka tsagaita wuta, ai cikin sati daya suka dawo da daliban bayan an tsagaita wutar.

“To idan har za a iya kulla yarjejeniyar tsagaita wuta ta sati daya, don me ba za a kulla tsagaita wuta ta daina yakin gabadaya ba, yadda za su fito a daina yakin haka nan?”

Da yake jawabi, shugaban Kwamitin Mashawartan Kungiyar ta Jinkai, Auwal Rafsanjani, ya ce kungiyar ta su ta na taimakawa ne domin jama’a su fito su san ‘yancin su.

“Kungiyar Jinkai ta Kasa da Kasa ba ta fito ta na gasa da kowane bangare ba ne. kawai ita ta na aiki ne domin tabbatar da cewa ana kare wa kowane dan Najeriya ‘yancin sa.”

“Ganin irin hujjojin da muke da su ne ya sa muka kawo wasu daga cikin wadanda aka ci wa zarafin domin a ji daga bakin su,

“Don me wasu za su rika cewa mu na kokarin rikita Najeriya? Mu fa mu na nuna wa gwamnati ne cewa ta fito ta yi abin da ya dace ta yi wajen kare hakkin ‘yan Najeriya.”

‘YAN MAJALISA SUN CE WANI ABU

Sani Zorro, wanda shi ne Shugaban Kwamitin Majalisar Tarayya a kan Sansanoni da ‘yan gudun hijira, ya ce duk ta inda aka buga aka buga, to ana daina yaki ne ta hanyar sasantawa.

“Tunda dai mun kasa ganin karshen wadannan Boko Haram a cikin sama da shekara biyar, to ya kamata a samu wata hanyar kawo karshen wannan fitina.” Inji Zorro.

“Shin wai ku na tsammanin kashe-kashen da ake fama da su a jihar Kaduna da Zamfara duk ba su da alaka da Boko Haram ne? Ai yanzu Najeriya ta na takara ne da kasar Syria wajen fattatakar jama’a daga matsugunan su.”

Shi kuwa Sanata Shehu Sani, cewa ya yi bai kamata gwamnati ta yi watsi da rahoton Kungiyar Jinkai ta Duniya ba.

“Ana yawan cin zarafin mata, kuma wannan abin takaici ne. kuma wannan rahoto bai dora wa gwamnati laifi ba, abin da ake fama da shi ne a kasar nan.

Ya ce abin takaicin kuma shi ne jami’an gwamnati ba su ma tsaya sun karanta rahoton ba, saboda hankalin su kawai ya karkata ga zabe, sai suka fara bobbotai kawai.

“Idan dai har gwamnan da ke kan mulki a yanzu ba kunya ba tsoron Allah har ya ce wai kashe-kashen da ake yi a Arewa duk zuguguta shi ne ake yi, bai taka kara ya karya ba, to ana cikin mummunan matsala fa.”

Share.

game da Author