Yadda na zama mai wa’azi a kurkuku – Jang

0

Tsohon Gwamnan Jihar Filato Jonah Jang, wanda aka bayar da belin sa jiya Alhamis, ya bayyana yadda ya yi rayuwa tsawon mako guda a cikin kurkukun Jos.

Ya ce zaman da ya yi haramtacce ne wanda kotun ta tura shi ba bisa ka’ida ba.

An daure shi ne a kan zargin salwantar naira biliyan 6.3 a lokacin da ya ke gwamnan jihar Filato.

“Idan da har dokokin kasar nan su na aiki a karkashin wannan gwamnatin, to tsarewar da aka yi mini tauye hakki na ce matuka. Ina magana kan hakkin da dokar 1999 ta ba ni.”

Haka ya bayyana a cikin wata takarda da ya fitar kuma ya sa wa hannu da kan sa bayan an bayar da belin sa a kan kudi naira milyan 100.

“EFCC ta tsare ni sama da tsawon mako guda aka hana ni ‘yanci na, maimakon awa 24 da doka ta ce ta tsare ni.

“Doka ta ce bayan kwana daya tal da kama wanda ake zargi, to a tura shi kotu, amma sai da EFCC ta tsare ni sama da mako daya. Don haka lauya nay a shigar da kara kotu, kuma zai bi mini hakki na.

Amma a matsayi na wanda ya yi amanna da Isa Almasihu, na dauki wannan abu a matsayin abin farin ciki. Kuma na samu damar yin wa’azi ga yawan daurarrun da na samu a gidan kurkuku.

A masayin na na gwamnan da aka dama min amanar jiha, na gudanar da ayyukan inganta rayuwar al’umma, kuma ha daukaka jiha ta da al’ummar ta kamar yadda aka kyautata zaton ana so a ga na yi.

A karshe ya ce bai rike kowa a zuciyar sa ba.

Idan ba a manta ba, a wata hira da ya yi, ya ce har gadon da Obasanjo ya kwanta a kurkukun Jos, shi ma sai da ya kwanta a kai.

Share.

game da Author