Yadda ake safarar baliban sakandare zuwa kasar Libya -Jami’i

0

Akalla an yi lodin daliban sakandare 100 daga Sakandaren Idogbo da ke Benin a jihar Edo zuwa kasar Libya a cikin watanni hudu.

Babban Mataimakin Gwamnan Jihar Edo a kan magance safarar mutane mai ne ya bayyana haka, mai suna Solomon Okoduwa.

Okoduwa ya kara da cewa wasu malaman makarantar ne suka tabbatar masa da haka, su na kokawa da cewa a yanzu makarantar ta zama dandalin safarar daliban sakandare zuwa kasar Libya.

Daga nan sai yay i gargadin cewa gwamnati ba za ta yarda wannan laifi ya ci gaba da dorewa ba.

Ya kuma gargadi daliban makarantar da su guji rudin da ake yi musu romon-kunne a na rudar su ana kai su Libya da nufin samun abin duniya.

Ya ce zuwa Libya ko Turai tafiya ce mai tarin hadari, kuma haramtacciyar hanya ce.

Yawanci kamar yadda ya kara jaddada musu, tafiya ce da akasari mutuwa ke riskar wasu tun a cikin dajin Sahara.

Idan kuma an yi sa’a har an shiga jirgin ruwa, to nan ma ana haduwa da hadurran cikewar jiragen a cikin teku.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa, NAN ya ruwaito cewa an dawo da akalla matasa 3400 a cikin watanni shida daga Libya.

Share.

game da Author