WATANDAR KUDIN NAJERIYA: Obasanjo da su Jonathan za su hadu da fushin Allah – Buhari

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya sake dira a kan shekaru 16 da gwamnati jam’iyyar PDP ta shafe ta na mulkin kasar nan, tsakanin 1999 zuwa 2015, ya na mai cewa Allah zai yi musu hisabi daidai da tabargazar da suka tafka wajen almubazzaranci da dukiyar Najeriya.

“Yan Najeriya sun san cewa a baya babu titina, babu hanyoyin jirgin kasa, babu hasken lantarki duk kuwa da biliyoyin dalolin da suka ce sun kashe wajen samar da wadannan ababen more rayuwa. Allah ne kadai zai yi musu hisabi a kan abin da suka yi.”Inji Buhari.

Shugaba Buhari ya tuntubi Gwamnan Babban Bankin Najeriya, jim kadan bayan an rantsar da shi, inda ya ce masa ai babu kudi a cikin asusun gwamnatin tarayya.

Daga nan ya ci gaba da cewa abin takaicin kuma shi ne, babu wasu ababe ko ayyukan ci gaba da aka yi, wadanda za a iya nunawa a ce a kan su ne aka karkashe makudan kudaden da ribar danyen man fetur da suka tara a lokacin.

“A wancan lokacin cikin shekaru 16 da PDP ta yi ta na mulki, Najeriya na hako gangar danyen mai miliyan 2.1, kuma ana saida kowace ganga daya dala 100, a kowace rana. Amma lokacin da muka hau mulki, farashin danyen mai ya fadi warwas zuwa dala 37 zuwa 38, daga baya ya yi tsaye tsakanin dala 40 zuwa 50.

“Ni da kai nan a tashi na tafi Babban Bankin Tarayya. Ga ma gwamnan su nan a zaune. Na ce masa to kai me ake ciki ne? Ya dube ni ya ce babu komai sai ma tulin bashin da aka bar mana.

“Na ce masa kai tambayar ka fa na ke yi, ina kudin da ke cikin baitulmalin Najeriya? Ya ce ai ba komai.”

An tuntubi kakakin yada labaran PDP domin a ji ta bakin sa, amma wayar sa a kashe.

Share.

game da Author