Matan aure dake zama a kauyukan Egosi da Odo-Owa karamar hukumar Oke-Ero jihar Kwara sun koka kan yadda rashin ingantattun cibiyoyin kiwon lafiya a kauyukan su ya sa dole su koma yin amfani da Ungozoma na gargajiya a duk lokacin da dayan su za ta haihu.
Wadannan mata sun bayyana wa PREMIUM TIMES cewa lalacewa da rashin kayan aiki a Cibiyoyin kiwon lafiya da ke kauyukan su ne dalilan da ya sa suka koma amfani da dabarun gargajiya.
Matan sun ce suna da ungozoma na gargajiyya biyu a kayukan su, wani tsoho mai suna Kehinde Adebayo da ka fi sani da ‘Baba Apiri’ sannan da wata tsohuwa mai suna Janet Oyelowo ita ma da aka fi kira da ‘Mummy’.
A hira da suka yi da mu, Baba Apiri ya ce bashi da kwarewa na musamman kan abin da yake yi, ya tsunduma harkar ne kai tsaye da rana tsaka.
” Magungunan gargajiya ce kawai nake amfani da su wurin karbar haihuwa sannan da haka ne na koya wa matata da yaro na saboda duk dare mukan karbi haihuwa uku kafin gari ya waye.”
Ita kuwa Mummy ta bayyana cewa ta sami nata horon ne daga wasu kwararrun ma’aikatan lafiya amma duk da hakan maganin zazzabin cizon sauro kadai take badawa idan har mai haihuwa na bukata.
” Wata kawata ce take taimaka mini a duk lokacin da mata suka zo haihuwa wurina sannan idan haihuwa ya zo mana da tangarda mu kan aika da mace babbar asibitin dake cikin gari domin ta samu kulan da ya kamata.
Duk da haka mummy ta ce babu wanda sukat taba aikawa babbar asibitin tun da suka fara karbar haihuwa a kauyen.
Bayan tattauna da mukayi da wadanan unguwan zoma biyu munyi tattaki zuwa wasu cibiyoyin kiwon lafiya a wannan kauyuka inda muka gani wa idanuwar mu cewa lallai wadannan asibitoci na nan a wulakance.
Ma’aikatan da muka tattauna da su sun koka kan nuna halin ko-in-kula da gwamnati take yibwa Cibiyoyin Kiwon Lafiya a wadannan wurare.
Sun koka da rashin, gyara asibitocin, rashin magani, likita da sauran su.
Discussion about this post