Tilas masu neman shiga aikin dan sanda su rubuta jarabawar JAMB

0

Hukumar ‘Yan sanda sun tabbatar da cewa dukkanin masu neman shiga aikin kurtun dan sanda tilas sai sun zauna sun rubuta jarabawar JAMB tukunna.

Shugaba Muhammadu Buhari ne ya bada umarnin a gaggauta daukar sabbin ‘yan sanda 6,000 domin samun kari a kan 300,000 da ake da su.

A cikin wata takarda da Kakakin Hukumar na Kasa, Jimoh Mosheed ya sa wa hannu, an bayyana cewa: “A karon farko ba za a dauki kowa ba sai idan bayan an kammala tantancewa kuma an zauna wata jarabawar gwaji, inda kowa zai rubuta jarabawar JAMB, domin a samu hazikai sosai.”

Sauran ka’idojin da kowace jiha za ta cika, sun hada da cewa Sufeto Janar ya sanar da cewa a tabbatar kowace jiha 36 har da cikon Abuja su tantance wadanda za a dauka a ranar 7 Ga Mayu, 2018.

Sanarwar ta kara da cewa za a yi wa kowa gwajin cutar kanjamau, sannan mata za a hada da yi musu gwajin ciki sai kuma rubuta jarabawar JAMB.

Ya kuma hori jami’an shirya jarabawa da tantancewa da su tabbatar babu nuna son kai ko bangaranci ko nuna fifikon wanda bai cancanta ba a kan wanda ya cancanta.

Sannan kuma za a yi wa kowa gwajin idanu domin a tantance masu gani garau da kuma masu gani garara-garara. Har ila yau za a gane masu iya karanta rubutu a kusa da masu iya karanta sai wanda ke daga nesa.

Za a kuma auna kowa domin a gano mai ciwon suga, hawan jini, cutar Tibi da sauran su.

Akwai kuma gwaji da bincike na kwakwalwa domin a gano ko wani ya na da gadon tabin-hankali, sai kuma tambayoyin kwakwaf domin gano kwarkwantacce da wadanda suka fara zautuwa sabili da ‘yan shaye-shayen zamani ko masu amfani da jibaga a boye.

A karshe an yi kira ga daukacin jama’a da kuma masu neman shiga aikin da cewa, duk wanda ya gani ko ya ji ana neman aikata ba daidai ba dangane da wannan gagarimin shiri, to ya gaggauta kiran daya daga cikin wadannan lambobi da ke kasa:

08076036011, 08037036257, 08034360919, 08037855951, 08065823054, 08036753589.

Share.

game da Author