Tarayyar Turai za ta tallafa wa ‘yan Najeriya 7,831 da suka dawo daga Libya

0

Kungiyar Tarayyar Turai wadda ya zuwa yanzu ta yi dalilin dawowar ‘yan Najeriya 7,7720 daga Libya da wasu kasashen waje.

Jakadan Tarayyar Turai kuma shugaban tawaga zuwa Najeriya, Ketil Karlson ne ya bayyana haka a lokacin ganawa da manema labarai a jiya Laraba a Abuja.

Ta ce akwai karin wasu 111 da za su iso Najeriya a yau Alhamis ta jirgin saman Murtala Mohammed da ke Lagos.

Karlson ya kara da cewa kashi 50 bisa 100 na wadanda suka dawo din ‘yan jihar Edo ne, yayin da wasu kashi 15 cikin 100 kuma daga jihar Delta..

Daga nan sai ya kara da cewa dukkan wadanda suka amince suka dawo gida ta hanyar tsarin Kungiyar Tarayyar Turai da kuma Kungiyar Kula da Masu Gudun Hijira, to za a tallafa musu da kudaden da za su taimaki kan su wajen sake lalen rayuwar su, domin su tsira da mutuncin kan su.

Da wannan ne ya ce za kuma a ba su horo da dabarun yin sana’o’in hannu domin su samu sana’o’in dogaro da kan su.

Share.

game da Author