AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW.
Hadisi Da’ifi shi ne dukkan Hadisin da ya gaza cika sharuddan ingacin karban Hadisi. Da’ifi ya kasu zuwa gida biyu, Da’ifin da ake aiki dashi da kuma wanda ba’a aiki dashi. Shi Da’ifin da ake aiki dashi ana kiran sa Hasanun li Gairihi: wato Hadisin da aka ruwaito ta hanyoyi dayawa, amma dukkanin hanyoyin masu rauni ne, sai dai yawansu yana daga darajar Hadisin zuwa Hasanun li Gairih.
A takaice shi Hadisi Da’ifi ba nau’i daya bane kuma kuma ba daraja daya bane, misali: Hadisi Da’ifi bisa raunin haddar mai ruwaya, ba dai-dai yake da Hadisi Da’ifi bisa karyar mai ruwaya ba.
Imam Ibn Hibban ya lissafa nau’ukan Hadisi Da’ifi har nau’i 49, kuma kowanne daga cikinsu yanada daraja mabambanciya.
Malamai sun kasu gida uku akan aiki da Hadisi Da’ifi:
1. Kashi na farko sun tsaya akan cewa ba’a aiki da Hadisi Da’ifi dungurungum a cikin komai na shari’a, hukunci ne ko falalace. Wannan ita ce mazhabar Imam Bukhari, da Imam Muslim da Ibn Hazm da Ibnul Arabi da Ibn Taimiyya, da Albani. Dalilinsu shi ne Hadisi Da’ifi zato ne, kuma Qur’ani da Hadisi sun hana aiki da zato.
2. Kashi na biyu kuwa sun tsaya akan cewa ana aiki da Hadisi Da’ifi kai tsaye, matukar ya cika wasu sharuddan da zamu ambata nan gaba.
Kuma wannan shi ne mazhabin Imam Abu-Dauda, da Imam Ahmad, da Imam Suyudi. Suna ganin Da’ifancinsa baya koresa daga cikin Hadisai, kuma yafi ra’ayin wani mutum daraja.
3. Mazhabin karshe shi ne ana aiki da Hadisi Da’ifi ne a cikin halal da haram, wajibi da farilla ko falala, kwadaitarwa da tsoratarwa da sauran su. Amma fa idan raunin nasa ba mai tsanani bane, kuma babu waninsa Wannan shi ne matafiyan malaman fiqihu guda hudu da Imam Ibn Hajar.
SHARUDDAN
1. An ijima’in cewa ba’a aiki da Hadisi Da’ifi acikin abinda ya shafi Aqida ko Tauhidi.
2. Idan Hadisi Da’ifi bai ci karo da aya ko ingantaccen hadisi ba.
3. Idan da’ifancin sa ba mai tsanani bane.
4. Idan Hadisin bai zo da wani sabon abo ba.
5. Kuma kar a kudirci tabbatuwarsa da jinginasa zuwa ga Annabi SAW.
Allah ka datar da mu zuwa ga alheri kuma ka bamu alherin duniya da lahira. Amin
Discussion about this post