Fitaccen malamin addinin musuluncin nan kuma attajiri mazaunin garin Kano Isyaka Rabiyu ya rasu yau a birnin Landan.
Kamar yadda Kamfanin dillancin Labarai ta ruwaito, Shehin malamin ya rasu ne bayan ‘yar gajeruwar rashin lafiya da yayi fama da ita.
Za a yi jana’izar Sheikh da zaran an dawo da gawar sa kasa Najeriya.
Ya rasu ya bar ya’ya da dama cikin su akwai Abdussamau Isyaka Rabiu, shugaban Kamfanin Bua, Rabiu Rabiu, shugaban Kamfanin jirgin sama na IRS da sauran ‘ya’ya da yawa.
Ya rasu yana da shekaru 90 a duniya.