SERAP ta aika wa Majalisar Dinkin Duniya kukan yadda Buhari ke yawan fatali da umarnin kotu

0

Kungiyar Rajin Kare Hakki da Tabbatar da Adalci, SERAP, ta rubuta wa Majalisar Dinkin Duniya kakkausar wasika, inda ta ke nuni da irin yadda Shugaba Muhammadu Buhari ke take dokar kasa, wadda ya rantse zai kare, wajen kin bin umarnin kotu.

Kungiyar ta ce, “irin yadda Buhari ke tsame umarnin da ya ga dama da ga kotu ya bi, da kuma wadanda ya ke dannewa, hakan wata mummunar alama ce mai nuna cewa an jefa doka da oda cikin aljihu kawai.

A cikin wata takardar korafi da SEREAP ta aika wa Majalisar Dinkin Duniya, a ranar 11 Ga Mayu, ta ce irin yadda gwamnatin Najeriya ke karya doka ta hanyar kin bin umarnin kotu, alama ce ta datse kafafun da karfinn ikon da doka ta ke da shi a kan ko ma wane ne.

Sannan kuma hakan na kara tauye cin gashin kan da kotuna ke da shi kwarai, wanda idan ba a yi saurin taka wa matsalar burki ba, to hatta batun yaki da cin hanci da rashawa da ake cewa ana yi, zai koma Bulkara kawai.

“Gwamnatin Najeriya ta ki bin umarnin kotu da sau da dama ta ce a saki shugaban mabiya shi’a da ke tsare, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da ke tsare tun cikin watan Disamba, 2015 tare da matar sa Zeenat.

Baya ga kin bin umarnin kotu a saki Zakzaky, cikin watan Maris, 2016, Mai Shari’a Mohammed Idris ya umarci gwamnatin tarayya da ta buga yadda aka kashe makudan kudeden da gwamnatin tarayya ke kwatowa daga hannun wadanda suka wawure kudaden, tun daga 1999, amma shiru gwamnatin Buhari ba ta yi ba.

Ita ma Mai Shari ta Hadiza Rabiu ta bayar da wannan umarni, amma aka biris da ita.

Share.

game da Author