Buhari yayi ganawar sirri da Saraki da Dogara

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki da Kakakin Majalisar tarayya, Yakubu dogara.

Sai dai kuma ganawar ta su ta kasance ne a cikin sirri. Sun gana na kankanen lokaci bayan komawar Buhari Abuja daga Daura, inda ya je domin halartar zaben shugabannin mazabun jam’iyyar APC.

Bayan sun fito daga tattaunawar, Saraki ya shaida wa wakilan jaridu na Fadar Shugaban Kasa cewa sun je ne a bisa gayyatar shugaban da kan sa.

Ya ce Buhari ya ba su bayanin abin da ya wakana a ziyar da ya kai wa Shugaba Donald Trump na Amurka a makon da ya gabata.

Ya kara da cewa sun kuma yi magana dangane da kasafin kudi na 2018.

Sai dai kuma tun cikin makon da ya gabata ne majalisar ta ce za ta tura wa Buhari kasafin kudin a gobe Talata.

Saraki ya kuma kara da cewa, “mun kuma yi magana dangane da abin da ya shafe mu, shigar-kutsen da aka yi wa Majalisar Dattawa, wanda shugaban shi ma ya nuna damuwar sa, kuma ya ce za a ci gaba da bincike da daukar mataki, domin abin da ya faru inji shi, cin zarafin Najeriya ne gaba daya ba majalisar kadai ba.”

Dangane da kasafin kudi na 2018 kuwa, ya ce su na sa ran maida wa shugaban kasa shi a farkon mako mai shigowa.”

Daga nan kuma Saraki ya kara da cewa sun tayar wa shugaban kasa korafin su da Sufeto Janar na ‘Yan sanda, Ibrahim Idris, dangane da kememen da ya yi ya ki bayyana a gaba majalisa har sau biyu bayan sun gayyace shi.

Sun nuna takaicin yadda babban mai kare dokoki da kuma hana aikata laifuka shi ne zai karya dokar kasar da ya yi alkawarin zai kare.

YAKUBU DOGARA

A nasa jawabin Dogara ya ce sun tada batun Sanata Dino Melaye da ke tsare a hannun jami’an ‘yan sanda kuma ya na fama da jiyya. Sun shaida wa shugaban kasa ana tuhumar Dino ne da zargin mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.

Dogara ya nuna rashin jin dadin irin yadda ‘yan sandan kasar nan ke aiki kamar zamanin mulkin jahiliyya, inda banda karfa-karfa da musgunawa ba a komai.

“Ba mu ce duk wanda ake zargin ya karya doka kada a tuhume shi ba. Amma dai a ce an tura wanda ake tuhuma zuwa kotu a kan keken daukar marasa lafiya a asibiti, to wannan bai nuwa cewa dikoradiyyar mu wata abar koyi ba ce.

“Kai idan ma har Dino Melaye karya ya ke yi, lafiyar sa kalau, kawai bagalo ya yi don a ce ba shi da lafiya kamar yadda wasu kafafen yada labarai ke nunawa, ai duk daren dadewa ko ba-jima ko ba-dade, zai gaji da zaman asibiti. Kuma ba gudu zai yi ba.” Inji Dogara.

Share.

game da Author